Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya aike da sakon taya murnar bude taron baje kolin albarkatun ruwa
2019-10-15 15:49:05        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga taron baje kolin albarkatun ruwa na kasar Sin na bana, wanda aka bude yau Talata a birnin Shenzhen dake lardin Guandong na kudancin kasar Sin.

Cikin sakon, shugaba Xi, ya ce tekuna na taka gagarumar rawa ga kasancewar bil Adama da kuma ci gabansu.

Ya kuma bukaci a yi kokarin inganta hada wurare ta ruwa da kuma hadin gwiwa a dukkan bangarori, tare da kulla dangantaka kan harkokin ruwa tsakanin dukkan kasashe. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China