Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Sin za ta nacewa ga manufar raya dangantakar kut da kut tsakaninta da Indiya
2019-10-12 20:53:31        cri

Yau Asabar a birnin Chennai, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Indiya Narendra Modi, inda ya nuna cewa, Sin za ta nacewa ga manufar kiyayewa da kuma raya dangantakar kut da kut tsakanin kasashen biyu. Kuma ya nanata cewa, shekaru masu zuwa sun kasance muhimmin lokaci na farfado da al'ummar Sinawa da Indiyawa, haka kuma muhimmin lokaci ne na zurfafa dangantakar kasashen biyu. Ya ce kamata ya yi, bangarorin biyu su tsai da wani tsari tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare da hangen nesa don raya dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata, da cimma muradun farfado da al'umomin kasashen biyu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China