Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya mika sakon taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar kungiyar yara ta kasar Sin
2019-10-13 16:13:30        cri

Albarkacin cika shekaru 70 da kafuwar kungiyar yara ta kasar Sin, babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin soja na kwamitin tsakiya Xi Jinping ya mika sakon taya murnar, a madadin kwamitin tsakiya na JKS, ya taya miliyoyin yara 'yan kungiyar da wadanda suke aikin ba da taimako ga sha'anin yara a kasar Sin kurna tare da mika musu sahihiyar gaisuwa.

A cikin sakon da ya bayar, Xi Jinping ya ce, a cikin wadannan shekaru 70 da suka gabata, kungiyar ta nace ga ka'idar hada aikin samun ilmi daga kungiya da samun ilmi daga ko'ina da gwajin aiki bisa fasaha da ake da shi waje guda, ta yadda za a ba da gudunmawa ga raya sha'anin jam'iyya da jama'a daga zuriya zuwa zuriya.

Kungiyar yara ta kasar Sin na karkashin jagoranci jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wadda take da mambobi fiye da miliyan 130 da shekarun haifuwarsu tsakanin 6 zuwa 14. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China