![]() |
|
2019-10-14 10:33:47 cri |
Shugabar kasar Nepal Bidya Devi Bhandari ta shirya kasaitaccen bikin ban kwana da shugaba Xi a filin jirgin saman kasar. Inda Xi ya bayyana ziyararsa a kasar Nepal a matsayin cikakkiyar nasara, Xi ya shedawa Bhandari cewa tun bayan isowarsa, ya samu kyakkyawar tarba daga gwamnatin Nepal da al'ummar kasar.
Shugaba Xi ya ce ya gamsu cewa, ana ta sada zumunci a tsakanin Sin da Nepal, kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ba zata taba rushewa ba.
Kana ya yi kira ga bangarorin biyu da su kara kaimi wajen cigaba da kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Bhandari a nata bangaren ta ce, ziyarar da shugaba Xi ya kai kasar mai cike da nasarori da alfanu ta kasance muhimmin al'amari a tarihin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Dangantakar dake tsakanin Nepal da Sin ta shiga wani sabon babi a bisa matsayin koli, in ji Bhandari, ta kara da cewa, Nepal za ta yi aiki tare da kasar Sin wajen daga matsayin kyakkyawar dangantakar makwabta dake tsakanin kasashen biyu da ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China