Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gana da takwararsa ta kasar Nepal
2019-10-13 16:34:58        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwararsa ta kasar Nepal Madam Bidhya Devi Bhandari a fadarta dake Katmandu a jiya Asabar. Shugabannin biyu sun sanar da kara hadin kansu da cin moriya tare don raya dangantakar abota daga zuriya zuwa zuriya bisa manyan tsare-tsare dake iya kawo bunkasuwa da wadata ga kasashen biyu.

Yayin ganawar tasu, Xi ya jaddada cewa, kamata ya yi bangarorin biyu su karfafa da kuma inganta tushen dangantakar kasashen biyu a siyasance, da ayyana aikin raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya a matsayin muradun da kasashen biyu za su cimma nan gaba. Sin za ta ci gaba da goyon bayan kokarin da Nepal take yi na kiyaye 'yancin kan kasar da ikon mallakar kasar da cikakken yankin kasar, tare kuma da ba da taimakon da ya dace gwargwadon karfinta kan bunkasuwar tattalin arziki da al'ummar kasar. Ya kara da cewa, ya kamata bangarorin biyu su kafa tsari mai kyau wajen hadin kai a dukkan fannoni da kafa tsarin yanar gizo ta Intanet tsakaninsu da kuma habaka hadin kansu da yin mu'amala a dukkanin fannoni.

A nata bangare, Bidhya Devi Bhandari ta ce, kasashen biyu na sanar da kafa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare, matakin da zai karfafa dankon zumuncinsu kwarai da gaske, da kuma sa kaimi ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. Nepal na godiya sosai ga taimakon da Sin take ba ta cikin dogon lokaci, kasar na mutunta ikon mallaka da cikakken yankin kasar Sin, ba za ta yarda da kowane irin yunkurin nuna adawa ga kasar Sin ba.

Daga baya kuma, a cikin ganawarsa da firaministan kasar Khadga Prasad Sharma Oli, Xi Jinping ya nanata cewa, ko wani mutum na son kawo barakar kasar Sin, kaikai zai koma kan mashekiya, kuma ko wani yunkurin da kasashen waje suke yi na kawo barakar kasar Sin aikin banza ne. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China