Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Kamata ya yi Sin da Indiya su yi kokarin amfanawa juna da cin moriyar juna
2019-10-12 21:01:44        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Indiya Narendra Modi a yau Asabar, inda ya nuna cewa, kokarin amfanawa juna da cin moriyar juna hanya ce daya tilo da kasashen biyu za su bi, matakin da ya dace da bukatun jama'ar kasashen biyu. Ya ce, kamata ya yi a fahimci bambanci dake tsakaninsu, kuma kada a mai da shi tarnaki ga hadin kan kasashen biyu. Sin na fatan samun bunkasuwa yadda ya kamata, a hannu guda kuma, tana fatan ganin ita ma Indiya ta samu bunkasuwa mai armashi.

Xi Jinping da Narendra Modi sun cimma daidaiton cewa, dole ne kasashen biyu su daidaita bambancin ra'ayi a tsakaninsu yadda ya kamata. Narendra Modi ya ce, ya kamata kasashen biyu su kara dankon zumunci tsakaninsu don bude wani sabon babi a dangantakarsu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China