Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ziyarar shugaba Xi a Asiya ta Kudu ta bude sabon shafin hadin gwiwar yankin, in ji Wang Yi
2019-10-14 14:12:05        cri

Daga ranar 11 zuwa 13 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron ganawar shugabannin kasashen Sin da Indiya karo na biyu, da kuma kai ziyarar aiki a kasar Nepal, bisa gayyatar da kasashen biyu suka yi masa. Cikin wadannan kwanaki uku, shugaba Xi ya halarci taruka da dama, wadanda suka ja hankalin kafofin watsa labarai na kasashen ketare, saboda a ganinsu, ziyarar shugaba Xi tana da muhimmiyar ma'ana cikin tarihin kasashen. Bayan ziyarar tasa a kasashen, mamban majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya fidda karin bayani dangane da ziyarar Shugaba Xi Jinping na wannan karo.

Wang Yi ya ce, jagoranci na shugabannin kasashen biyu ya bada tabbaci kan bunkasuwar dangantaka a tsakanin Sin da Indiya. A yayin da yake ziyarar aiki a kasar Indiya, shugaba Xi ya yi shawarwari mai zurfi da firaministan kasar Indiya Narendra Modi. Shugaba Xi ya jaddada cewa, zurfafa zumunci da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Indiya ya dace da moriyar kasashen biyu, da ma al'ummomin kasashen biyu, zai kuma bada gudummawa ga zaman lafiya da bunkasuwar kasa da kasa na dindindin. Ya kamata kasashen biyu su yi shawarwari kan manyan batutuwa cikin lokaci, da girmama moriyar bangarorin biyu, da kara fahimtar juna dake tsakaninsu, domin ci gaba da warware sabanin dake tsakaninsu. Kasar Sin tana son neman ci gaba, tana kuma fatan kasar Indiya za ta sami ci gaba cikin yanayi mai kyau.

A nasa bangaren, Firaminista Modi ya nuna yabo matuka kan ra'ayin shugaba Xi, ya kuma bayyana cewa, ya kamata kasashen biyu su kula da moriyar juna, warware sabanin dake tsakaninsu yadda ya kamata domin raya dangantakar dake tsakaninsu zuwa dangantakar abokantaka, ta yadda za a bude sabon shafi na huldar dake tsakanin Sin da Indiya.

Haka kuma, shugaba Xi da firaminista Modi sun cimma ra'ayi daya kan zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu. Sun tsaida kudurin kafa tsarin mu'amalar tattalin arziki da cinikayya a kasashen biyu, da karfafa hadin gwiwar kasashen biyu kan daidaita manufofin raya tattalin arziki, da tattaunawa kan kafa dangantakar abokantaka a fannin masana'antu, domin inganta dauwamammen ci gaba na cinikayyar kasashen biyu. Kana, sun nuna fatan kulla "yarjejeniyar dangantakar abokantaka ta tattalin arziki bisa dukkan fannoni" da sauri, domin inganta musayar dake tsakanin kasashen yankin.

Bugu da kari, a yayin da suke tsokaci kan kariyar ciniki, sun nuna goyon bayansu kan tsarin cinikin dake tsakanin kasa da kasa da dokar kasa da kasa, domin tinkarar kalubalolin dake gaban kasa da kasa cikin hadin gwiwa.

Shugabannin biyu sun nuna yabo matuka kan sakamakon da suka cimma cikin ganawar tasu, suna son ci gaba da shawarwarin dake tsakaninsu a nan gaba. Kana bisa gayyatar da shugaba Xi Jinping ya yi masa, firaminista Narendra Modi zai sake kai ziyarar aiki a kasar ta Sin.

Bayan ziyarar tasa a kasar Indiya, shugaba Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a kasar Nepal. Dangane da wannan ziyara, Wang Yi ya ce, wannan shi ne karo na biyu da shugaban kasar Sin ya kai ziyara a kasar Nepal bayan ziyararsa ta farko yau shekaru 23 da suka gabata. Cikin ziyarar aiki ta wannan karo, shugabannin kasashen biyu sun tsara wani shirin bunkasa dangantakar dake tsakanin kashen biyu, kana, bisa jagorancinsu, aka kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa kimanin guda 20, wadanda suka shafi fannoni daban daban na zaman rayuwar al'umma, lamarin da ya bude wani sabon shafi ga zumuncin dake tsakanin kasar Sin da Nepal.

Ziyarar ta wannan karo ta daga matsayin dangantakar dake tsakanin Sin da Nepal zuwa wani sabon matsayi, shugaba Xi Jinping da takwararsa ta kasar Nepal Vidya Devi Bhandari sun sanar da cewa, kasashen biyu za su kafa dangantakar abokantaka da yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare bisa ka'idojin taimakawa juna da cimma moriyar juna, domin neman ci gaba da farfadowar kasashen biyu.

Wang Yi ya ce, wannan sabuwar dangantakar da aka kafa tsakanin Sin da Nepal ta nuna yadda za a raya huldar dake tsakanin kasashen biyu a nan gaba, tare da karfafa tasirin da kasashen biyu za su yiwa yankin baki daya. Muna ganin cewa, al'ummomin kasashen biyu suna son karfafa zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, kuma, jam'iyyu da sassa daban daban na kasar Nepal sun cimma ra'ayi daya kan wannan batu.

Haka kuma, shugaba Xi da shugabannin kasar Nepal sun cimma ra'ayi daya kan yin hadin gwiwa wajen hada manufar hada kan kasa da kasa ta hanyar hade hanyoyin mota da jiragen kasa da kuma shawarar "ziri daya da hanya daya", inda za su raya musayar kasashe ta hanyoyin motoci, jiragen kasa, jiragen sama da na sadarwa. Kana, Sin da Nepal sun sanar da fara yin nazari kan kafa layin dogo dake tsakanin kasashen biyu.

Haka zalika, a yayin ziyarar shugaba Xi a kasashen Indiya da Nepal, shugabannin kasashen biyu sun taya shugaba Xi Jinping murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, da kuma babban ci gaban da kasar Sin ta samu cikin shekaru 70 da suka gabata. A nasa bangaren, Xi Jinping ya yi bayani kan fasahohin kasar Sin na neman ci gaba, tare da yin bayani kan burin Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin na neman bunkasuwar kasa da kuma yin musayar ra'ayoyi da shugabannin kasashen biyu kan yadda ake gudanar da harkokin kasa da dai sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China