Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Turkiyya da Rasha da Iran dun tattauna batun tsaron Siriya
2019-09-17 10:33:25        cri
Shugabannin kasashen Turkiyya da Rasha da Iran sun gana jiya Litinin a birnin Ankaran kasar Turkiyya, inda suka tattauna batun tsaro a kasar Siriya, da jaddada bukatar tsagaita bude wuta a yankin Idlib dake arewa maso yammacin kasar.

Shugaba Recep Tayyip Erdoğan na Turkiyya, da Vladimir Putin na Rasha gami da shugaba Hassan Rouhani na Iran sun gudanar da taron koli a karkashin tsarin Astana. A yayin taron manema labarai da aka shirya, Recep Tayyip Erdoğan ya ce, tsanantar yanayin tsaron da ake ciki a yankin Idlib shi ne batun da shugabannin uku suka maida hankali a kai a shawarwarinsu. Tun watan Afrilun bana, fararen-hula kimanin dubu daya ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-hare ta sama da kasa da aka kai a yankin.

Erdoğan ya kara da cewa, ba za'a amince da irin goyon-bayan da ake nunawa 'yan ta'adda bisa hujjar yaki da kungiyar IS mai tsattsauran ra'ayi ba. Ya kamata Turkiyya da Rasha gami da Iran su kara daukar nauyin dake kansu wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar ta Siriya. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China