Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya isa Nepal domin ziyarar aiki
2019-10-12 20:35:20        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya isa birnin Kathmandu na kasar Nepal a yau Asabar. Wannan ne karon farko cikin shekaru 23 da wani shugaban kasar Sin ya ziyarci kasar ta kudancin Asiya.

Nepal muhimmiyar abokiyar huldar cinikayya da ayyukan ci gaba ce ta kasar Sin a kudancin Asiya, inda darajar cinikayya a tsakanin kasashen biyu ta kai dala biliyan 1.1, yayin da jarin da Sin ta zuba a Nepal, ya zarce dala miliyan 300 a bara. Haka zalika ana damawa da Nepal cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta kasar Sin.

Kasar Nepal ce kasa ta 2 a ziyarar da shugaba Xi ya kai kudancin Asiya, inda ya fara tsayawa a birnin Chennai na kudancin kasar India, domin ganawa karo na 2 da Firaministan kasar, Nerendra Modi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China