Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Ya kamata Sin da Indiya su zurfafa hadin kansu da cin moriya tare
2019-10-12 20:23:56        cri

Yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Indiya Narendra Modi a birnin Chennai, inda ya nuna cewa, ya kamata Sin da Indiya su yi amfani da damammaki masu kyau na kafuwar tsarin karawa juna sani tsakanin manyan jami'an bangarorin biyu ta fuskar ciniki da tattalin arziki, don hada tsare-tsaren raya tattalin arzikinsu waje guda, da tattaunawa kan yadda za su kafa dangantaka mai inganci kan sha'anin samar da kayayyaki. Ya ce Sin na maraba da kamfanonin Indiya na samar da magunguna da kimiyyar sadarwa su zuba jari a kasar.

A nasa bangare, Narendra Modi ya ce, Indiya na sa ran zurfafa hadin kai da kasar Sin a dukkanin fannoni, kuma kasar na maraba da kamfanonin kasar Sin su zuba jari a bangaren samar da kayayyaki da dai sauransu a kasar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China