Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gana da firaministan Indiya
2019-10-12 09:42:30        cri

Jiya Jumma'a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Indiya Narendra Modi a birnin Chennai na kasar Indiya.

A kofar wurin ibada na Mahabalipuram, da hannu bibbiyu ne, Narendra Modi ya yi maraba da shugaba Xi Jinping da ya kai ziyara a birnin Chennai. Xi Jinping ya ce, a shekarar da ta wuce, sun cimma nasarar ganawar tasu a birnin Wuhan na kasar Sin, inda suka daga dangantakar dake tsakanin Sin da Indiya zuwa wani sabon matsayi. Shugaba Xi ya kuma yi farin ciki sosai domin ziyararsa a jihar Tamil Nadu dake kudancin kasar Indiya, bisa gayyatar da firaminista Modi ya yi masa, domin zai kara fahimtarsa game da kasar Indiya.

A nasa bangare kuma, Mr. Modi ya ce, wurin ibada na Mahabalipuram shi ne kayan tarihi a fannin al'adu da aka gada daga kaka da kakannin kasar Indiya, ya duba mu'amalar al'adu da bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Indiya cikin karnuka da dama da suka gabata.

Sa'an nan, sun kalli rawar gargajiya ta Bharata da dai sauran raye-rayen gargajiyar kasar Indiya tare.

Sun kuma cimma ra'ayi daya cewa, ya kamata kasashen Sin da Indiya su mutunta juna, da koyi da juna domin neman ci gaba da farfadowar kasashen biyu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China