Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya isa kasar Indiya
2019-10-11 18:54:13        cri

A yau da rana ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Chennai dake kudancin kasar Indiya, inda zai yi ganawa karo na biyu da firaministan kasar ta Indiya Narendra Modi.

Yayin ganawar, shugaba Xi zai tattauna da Modi kan batutuwa masu muhimmanci na dogon lokaci da manya tsare-tsare kan alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Chennai dai, shi ne babban birnin jihar Tamil Nadu. Kuma yana gabar ruwan Bengal, kana cibiyar al'adu, tattalin arziki da ma ilimi ta kudancin kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China