Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin: Ya kamata bangarorin Syria su kai zuciya nesa don warware rikicin siyasar kasar
2019-08-08 11:01:02        cri
A jiya Laraba jakadan Sin ya bayyana cewa bangarorin dake rikici da juna a Syria ya kamata su kawar da dukkan sabanin dake tsakaninsu domin shiga tattaunawar lalubo bakin zaren warware rikicin siyasar kasar.

Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya bayyana wa taron kwamitin sulhun MDDr game da batun mutanen da ake tsare da su, da wadanda aka yi garkuwa da su, da ma wadanda suka salwanta a Syria cewa, ya kamata bangarorin Syria su yi la'akari da al'amurran da suka shafi makomar kasar, da muhimman bukatun jama'ar kasar, kuma su yi kokarin lalubo hanyoyin warware rikicin siyasar kasar ta hanyoyin da suka dace da yanayin Syria da hakkokin dukkan bangarorin kasar.

Da yake jawabi game da matsayar kasar Sin kan batun Syria, Wu ya ce, gwamnatin Sin ta damu matuka da yanayin ayyukan jin kai a kasar kuma ta damu da yanayin zaman rayuwar al'ummar kasar ta Syria.

Ya kamata al'ummar kasa da kasa su ci gaba da samar da taimakon kudade da kayayyakin tallafi ga jama'ar Syria, kana su taimakawa koakrin gwamnati da al'ummar Syria wajen sake gina kasar, a cewar wakilin na Sin. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China