Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jirgin saman tsaron Rasha ya tsallake hare haren jirage marasa matuka na 'yan tawayen Syria
2019-07-13 17:13:20        cri
Kamfanin dillancin labarai na SANA ya bada rahoto a jiya Juma'a cewa, jirgin saman tsaron kasar Rasha ya tsallake hare haren jiragen sama marasa matuka mallakar 'yan tawayen dake arewa maso yammacin kasar Syria.

Rahoton ya ce, jirgin saman tsaron na Rasha ya mayar da martani kan hare haren jiragen marasa matuka wanda kungiyoyin 'yan tawaye suka dauki nauyi a sansanin jiragen sama na Hmeimim dake arewa maso yammacin lardin Latakia a daren ranar Alhamis.

A cewar rahoton, an lalata jiragen saman marasa matuka uku daga wani waje dake da nisa daga sansanin jiragen saman, sai dai ba'a samu wata hasara ba.

Jiragen saman tsaron sun samu nasarar tsallake hare hare 10 wadanda mayakan 'yan tawayen dake lardin Idlib a arewa maso yammacin Syria suka yi yunkurin kaddamarwa a sansanin sojojin saman na Rasha, inji rahoton.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China