Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaminista Li ya jaddada muhimmancin wanzar da ci gaban tattalin arziki da kyautata rayuwar al'umma
2019-08-21 09:50:15        cri
Firaminista Li Keqiang, ya jaddada muhimmancin wanzar da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, tare da kara kyautata rayuwar al'umma. Mr. Li ya ce kara azama wajen aiwatar da gyare-gyare, da bude kofar kasar ga kasashen waje, da kirkire-kirkire, na da matukar muhimmanci wajen bunkasa ci gaban tattalin arziki da inganta rayuwar al'umma

Li, wanda kuma mamba ne a zaunannen kwamitin siyasa, na kwamitin kolin JKS, ya yi wannan tsokaci ne yayin da yake ziyarar aiki a lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin, ziyarar da ta gudana a ranekun Litinin da Talata.

Jami'an lardin dai sun shaidawa firaministan irin matakai da suke dauka, na inganta kwarewar ma'aikata a fannin sana'o'in hannu, suna masu cewa, sun tsara shirin bayar da horon sanin makamar aiki, ga al'ummun lardin da yawansu ya kai miliyan daya cikin shekaru 3 masu zuwa.

Game da hakan, Mr. Li ya jaddada muhimmancin sana'o'in hannu a fannin daga darajar masana'antun kasar Sin, yana mai kira ga cibiyoyin horas da sana'o'i sama da 2,000 dake sassan kasar, da su fadada daukar dalibai domin samar da kwararrun ma'aikata.

Yayin ziyararsa a sabon yankin raya tattalin arziki dake birnin Harbin, yankin da ya kyankyashe sabbin fasahohi da dama, firaminista Li ya ce jigon kara farfado da yankin arewa maso gabashin Sin, shi ne aiwatar da sauye-sauye, da kara bude kofa ga waje, da gudanar da kirkire-kirkire, kuma akwai bukatar kara azama wajen inganta muhallin gudanar da harkokin kasuwanci, da jawo karin masu fasahohi da za su bude sabbin ayyuka, masu nasaba da cinikayya da na kirkire-kirkire. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China