Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang ya fara ziyarar aiki a Rasha
2019-09-17 09:50:44        cri

Da maraicen jiya ne, firaministan Sin Li Keqiang ya isa birnin St. Petersburg don fara rangadin aiki a Rasha, bisa gayyatar takwaransa na kasar Rasha Dmitry Medvedev, gami da gudanar da shawarwarin firaministocin kasashen biyu karo na 24.

Li ya nuna cewa, duba da yadda duniya ke fuskantar sauye-sauye masu sarkakkiya gami da koma-bayan tattalin arziki, Sin na son karfafa hadin-gwiwa da mu'amala tare da Rasha a harkokin kasa da kasa, da kare ra'ayin kasancewar bangarori daban-daban da gudanar da cinikayya cikin 'yanci, a wani mataki na bayar da gudummawa ga raya tattalin arzikin duniya da tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa a shiyya-shiyya da ma duniya baki daya. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China