Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara amfani da hedkwatar CMG dake delta kogin Yangtse
2019-09-26 14:07:53        cri

 

Yau Alhamis, aka fara amfani da hedkwatar babban gidan rediyo da telibiji na kasar Sin (CMG) dake delta kogin Yangtse, wanda ya kasance hedkwata a wani yanki, kuma babbar tasha a wuri irinsa na farko na CMG, wato hedkwatar delta kogin Yangtse. Mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana direktan kwamitin JKS na birnin Shanghai Li Qiang ne ya kaddamar da wannan hedkwatar. Mataimakin shugaban sashen yayata manufofi na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban CMG Shen Haixiong da mataimakin direktan kwamitin JKS na birnin Shanghai, kana magajin birnin Ying Yong ne suka kaddamar da cibiyar fassara fina-finai da wasan kwaikwayo ta harsunan kasashe daban-daban na kasar Sin cikin hadin kai.

A cikin jawabinsa, Shen Haixiong ya ce, ran 26 ga watan Satumba na shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya CMG murnar kafuwarta da cika shekaru 60 da fara watsa shirye-shiryen telibiji a kasar Sin, inda ya jinjinawa ci gaban da CMG ta samu tun kafuwarta, tare kuma da karfafawa CMG gwiwar kafa wani babban dandali mai matsayin koli dake da karfin jagoranci da watsa labarai masu inganci dake da suna matuka a duniya. A cikin shekara daya da ta gabata, CMG ta samu ci gaba mai armashi.

Wannan hedkwata na da fadin muraba'in mita dubu 265. Wadda za ta kasance daya daga wasu sabbin alamomin birnin Shanghai, kuma za ta kai matsayin sansanin fina-finai na kasa da kasa mai matsayin koli a duniya, kuma cibiyar samar da al'adu da kirkire-kirkire mai inganci da cibiyar kawa ta kasa da kasa da wurin da jama'ar suke fi so. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China