Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban CMG ya gana da shugaban Reuters da mataimakin shugaban AP
2019-09-11 09:40:42        cri

A jiya Talata a nan birnin Beijing, mataimakin sashen yayata ayyuka na kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban babban gidan radiyo da telibijin na kasar Sin wato CMG Shen Haixiong, ya gana da shugaban kafar yada labarai ta Reuters Vredenburg, da mataimakin shugaban kawancen kafofin yada labarai na Amurka wato AP Bullard, wadanda suka halarci dandalin koli na hadin kan kasa da kasa dake hanyar siliki ta fuskar gidan telibijin na shekarar 2019.

Yayin ganawar tasa da Vredenburg, Shen Haixiong ya ce, babbar ka'ida da ma'aikatan CMG ke bi wajen yada labarai ita ce gaskiya, da adalci da daidaito. Ya ce CMG na fatan hadin kai da Reuters ta fuskar musanyar labarai, da more bayanan hada-hadar kudi, da yada labaran manyan batutuwa masu jawo hankalin kasa da kasa.

Yayin da ya gana da Bullard kuwa, Shen Haixiong ya ce, CMG zai ci gaba da zurfafa hadin kansa da AP, don koyi da juna da samun moriya tare. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China