Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi taron liyafar taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin, shugaba Xi Jinping ya ba da jawabi
2019-10-01 10:28:44        cri

A jiya Litinin da daddare ne aka shirya liyafar taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar kasar Sin a dakin taruwar kasar Sin.

Babban direktan kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin soja Xi Jinping ya halarci liyafar tare da ba da jawabi. Sinawa da kuma baki fiye da 4000 sun halarci taron don taya murnar.

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya nuna cewa, a cikin wadannan shekaru 70 da suka gabata, Sin ta yi kokarin samun ci gaba dake baiwa duk fadin duniya mamaki matuka.

Xi Jinping ya kara da cewa, kamata ya yi mu ci gaba da aiwatar da manufar 'kasa daya tsarin mulki iri biyu', da 'baiwa jama'ar yankin Hong Kong da Macao hakkin gudanar da harkokinsu'. Ya ce mun yi imani da cewa, yankin Hong Kong zai samu ci gaba, da makoma mai haske tare da babban yanki, saboda ganin goyon bayan da kasar ke bayarwa, da kuma kokarin da jama'ar yankin ke yi.

Ya ce ban da wannan kuma, ya kamata mu nace ga ka'idar kasar Sin daya tilo a duniya, da matsaya daya da babban yanki da Taiwan suka cimma a shekarar 1992, ta yadda za a ingiza bunkasuwar dangantakar yankunan biyu cikin lumana. Dinkuwar kasar Sin babban aiki ne da ba wanda zai iya hana shi. Kazalika, Xi Jinping ya nanata cewa, Sinawa na nacewa manufar diplomasiyya ta dogaro da kai, da samar zaman lafiya da hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, sannan kuma da ba da gudunmawarta wajen raya kyakkyawar makomar Bil Adama baki daya, da gaggauta sha'anin bunkasuwar Bil Adama cikin lumana. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China