Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya halarci bikin nune-nunen bayanan shaidar dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin a Rasha a cikin shekaru 70 da suka gabata
2019-09-30 11:02:15        cri

A jiya Lahadi a nan birnin Beijing, mamban majalisar gudanarwa ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, da jakadan Rasha dake kasar Sin Andrey Denisov, sun halarci bikin nune-nunen bayanan tunawa da cika shekaru 70 da kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Wang Yi ya nuna cewa, dangantakar kasashen biyu na samun bunkasuwa mai kyau da ya kai matsayin koli a tarihi, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu wato Xi Jinping da Vladimir Putin. Ya ce kamata bangarorin biyu su kara hadin kansu, da sauke nauyin dake wuyansu, na gudanar da harkokin duniya tsakanin bangarori daban-daban, da kare tsarin mulkin MDD, bisa la'akari da halin da duniya ke ciki na fuskantar sauye-sauye.

An ce, wannan biki ya nuna bayanai, da takardu, da kuma kayayyaki na tarihi masu daraja, da yawansa ya kai fiye da 60, abubuwan da suke shaida ci gaban da kasashen biyu suka cimma a baya a kokarin raya huldar dake tsakaninsu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China