Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ci gaba da kasancewa wurin dake sahun gaba a jawo jarin waje
2019-09-30 11:10:44        cri

A jiya Lahadi ne cibiyar yada labarai ta taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ta gudanar da taron gabatarwa mai takan "Bude kofa bisa sabon matsayi, da ingiza samun bunkasuwa mai inganci ta kasuwanci". Yayin taron, jami'in ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, Sin za ta samar da yanayin kasuwanci mai kyau ga kamfanonin waje, ta yadda za su zuba jari a kasar.

A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana, ministan kasuwanci na kasar Sin Zhong Shan, ya yi bayanin cewa, a cikin wadannan shekaru 70 da suka gabata, kasar Sin ta yi ta kokarin raya harkar zuba jari.

Zuwa yanzu, yawan jarin waje da Sin take yin amfani da su, da kuma adadin jarin da Sin take zubawa kasashen waje ya kai dala biliyan 138.3, da biliyan 143, adadin da ya kai matsayi na biyu a duniya.

Ya ce, Sin na zurfafa tsarin bude kofa ga kasashen waje bisa yankin gwaji na ciniki maras shinge, da tashar jiragen ruwa maras shinge, da dokar jarin waje da sauransu, matakin da ya sa Sin ta zama wuri da kasashen waje suka fi zubawa jari.

Mataimakin ministan kasuwanci, kana mataimakin shugaba mai jagorantar tawagar Sin a shawarwarin cinikin kasa da kasa Wang Shouwen, ya bayyana a gun taron cewa, kasuwa mai girma da Sin take da ita, na jawo hankalin kasa da kasa matuka. Ya ce, Sin na goyon baya kare hakkin kamfanonin waje a kasar Sin, da ci gaba da samar musu da hidima mai kyau. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China