Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
#China70# An shirya gagarumin bikin tunawa da cikar shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin
2019-10-01 10:26:42        cri

 

Yau Talata 1 ga wata, an shirya gagarumin bikin tunawa da cikar shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a dandalin Tian'an'men. Babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi a yayin bikin.

Bayan jawabin, za a gudanar da babban faretin soja, wanda a karon farko, sojojin Sin za su yi faretin soja a gaban jama'a bayan da aka yiwa rundunar gyaran fuska. Yawan sojojin da za su shiga faretin ya kai dubu 15, wanda ya kasance fareti mafi girma da aka yi a shekarun baya-baya nan. Bayan faretin sojan, za a kuma yi jerin gwanon jama'a da yawansu ya kai dubu 100. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China