Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An watsa wani tsohon fim mai alaka da kafuwar sabuwar kasar Sin shekaru 70 da suka wuce
2019-09-30 14:22:14        cri
Don taya murnar cikar shekaru 70 na kafuwar jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, da cika shekaru 70 na kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da kasar Rasha. A yau Litinin, an fara nuna wani fim da kamfanin telabijin da rediyo na kasar Rasha VGTRK, da babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG suka dauka tare, a cikin shirye-shiryen kamfanonin 2.

Fim din na kunshe da hotuna masu daraja, wadanda masu daukar fim na tarayyar Sobiet USSR suka dauka, a lokacin kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, wadanda suka shafi yadda aka gudanar da bikin kafa kasa, da muhimman tarukan da aka gudanar, gami da yadda mazauna birnin Beijing suka yi murna matuka a lokacin.

Saboda wasu dalilai na tarihi, ba a taba nuna wadannan hotuna cikin shekaru 70 da suka wuce ba. Sai dai zuwa wannan lokaci, manyan gidajen telabijin na kasashen 2 sun yi hadin gwiwa, inda suka gabatar da wannan fim mai daraja matuka. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China