Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala babbar muhawara a zauren MDD
2019-10-01 09:35:15        cri
A jiya Litinin ne aka kammala zaman babbar muhawara ta bana a zauren MDD, bayan da wakilai daga kasashen duniya 192 suka gabatar da jawabai a mumbarin majalissar, musamman game da muhimman batutuwa masu nasaba da hadin gwiwa don yaki da talauci, da samar da ilimi mai nagarta, da matakan kyautata yanayi, da gudanar da ayyuka cikin hadin gwiwa.

Cikin jawabinsa yayin zaman muhawarar, shugaban dandalin Tijjani Muhammad-Bande, ya ce ya gamsu da kiraye kirayen da aka yi game da aiwatar da manufofin cudanyar sassa daban daban, da na kyautata yanayi a zaman na wannan karo.

Ya ce yayin da yake sauraron masu gabatar da jawabai, ya gamsu da cewa daukacin sassa na tare da manufofin gudanar da cudanya tsakanin bangaroi daban daban.

Bande ya ce a duniya mai cike da rarrabuwa, hanya daya ta tabbatar da zaman lafiya da tsaro, da ci gaba mai dorewa, ita ce haduwar dukkanin sassa su yi cudanya da juna.

Shugaban ya ce ganin yadda kasashe mambobin majalissar 192 cikin jimillar 193 suka halarci babbar muhawarar ta wannan karo, ya nuna bukatar da kowane bangare na duniya ke da shi ga dan uwan sa.

Rahotanni sun nuna cewa, kasar Uzbekistan ce kawai ba ta gabatar da jawabi a yayin zaman na wannan karo ba.

Bisa tsarin zaman muhawarar dai, wakilin kasar Brazil ne farkon gabatar da jawabi, sai kuma na Amurka, kasar dake karbar bakuncin zaman. Yayin da kuma Sri Lanka ta kasance kasa ta karshe da ta gabatar da na ta jawabi a mumbarin zauren na MDD. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China