Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNHRC ta zartas da kuduri kan 'yancin raya kai
2019-09-28 16:52:10        cri
Majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD (UNHRC), ta zartas da kudurin kare 'yancin raya kai, da kungiyar kasashe 'yan ba ruwanmu (NAM) da kasar Sin suka gabatar tare.

Wannan kuduri ya jaddada cewa, 'yancin raya kai ya shafi kowa, kuma bai kamata a keta shi ba, ganin yadda kare 'yancin ke taka muhimmiyar rawa a kokarin cimma burin da aka sanya gaba cikin ajandar neman cigaba mai dorewa ta shekarar 2030. Haka zalika, kawar da talauci aiki ne mafi mihimmanci a kokarin tabbatar da 'yancin raya kai, da kuma neman samun ci gaba mai dorewa.

A cikin kudurin nan, an bukaci kasashe daban daban su nace kan manufar cudanya tsakanin sassa mabanbanta, da karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, don neman kau da shingen da ake fuskanta a kan hanyar neman samun ci gaba.

A nasa bangaren, Chen Xu, jakadan kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva gami da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, ya ce samun damar raya kai muhimmin sharadi ne dake bukatar a cika, kafin a samu tabbatar da cikakken 'yancin bil Adama. Kuma wata babbar matsala dake hana al'ummun kasashe masu tasowa tabbatar da 'yancinsu ita ce rashin ci gaban tattalin arziki. Ya ce, kamata ya yi, kasashe daban daban su yi kokarin neman samun ci gaba a lokaci guda, don aza harsashi mai karfi ga ayyukan kare hakkin dan Adam.

Kudurin kare hakkin raya kai da aka zartas a wannan karo wajen majalisar UNHRC ya samu goyon baya sosai daga kasashe masu tasowa, inda wakilansu sun bayyana cewa, hakki na raya kai na da matukar muhimmanci, kuma ta hanyar kare hakkin raya kai ne za a samu damar kare hakki na sauran fannoni. Saboda haka ya kamata sassa daban daban su kara zuba kudi ga aikin tabbatar da hakkin raya kai, da karfafa hadin kan kasashe daban daban a wannan fanni, gami da gaggauta samar da wasu takardun da za a iya yin amfani da su a matsayin dokokin kare hakkin raya kai. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China