![]() |
|
2019-09-22 15:38:54 cri |
Daraktan UNOSSC, Jorge Chediek, da Chen Daixing, mamba a kwamitin gudanarwa na kungiyar matasa ta Shenzhen ta kasar Sin ne suka sanar da shirin na horar da matasa 10,000, yayin taron matasa kan yanayi, wanda ya gudana a hedkwatar MDD.
Jorge Chediek, ya ce shirin zai dauki matakai kan kare yanayi ta hanyar kirkire-kirkire bisa tallafawa matasa masu sana'o'i dake rajin magance sauyin yanayi.
A cewarsa, shirin zai samar da hidimomin taimako ga sana'o'in da suka kafu da wadanda ke tasowa a kasashe masu tasowa.
Ya kara da cewa, shirin na da nufin horar da matasa masu sana'o'i 10,000 a cikin shekaru 5 ta hanyar inganta ilimi da samar da horo da samar da kudi da kirkire-kirkire da fasahohin zamani, yana mai cewa, shirin zai kuma tallafa wajen rayawa da bada jari da shawarwari ga dabarun kasuwanci 100. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China