Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na nacewa manufar cudanyar sassa daban daban, in ji Wang Yi
2019-09-27 20:31:39        cri
Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce kasarsa na nacewa manufar cudanyar sassa daban daban.

Mr. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin zantawarsa da babban magatakardar MDD Antonio Guterres, a gefen babban taron MDD karo na 74.

Ya ce manufar cudanyar sassa mabanbanta ita ce ta dace da zamani mai zuwa, yayin da manufar wariya ba za ta dore ba. Ya ce Sin na tare da MDD, da ma ingantaccen tarihin bil Adama. Minista Wang ya ce tarihi ba zai koma baya, ya goyi bayan lokacin da aka rika aiwatar da salon danniya ba.

Ministan ya kara da cewa, hanyar cudanyar sassa daban daban ita ce mai bullewa, duk da cewa dukkanin kasashen duniya na da ikon su, na neman ci gaba bisa yanayin da suke ciki.

Daga nan sai ya ce duba da cewa shekarar badi, ita ce ta cika shekaru 75 da kafuwar MDD, kasar Sin a shirye take ta yi amfani da wannan dama ta musamman, wajen habaka hadin gwiwa da MDD, domin tallafawa wajen gina rayuwa mai inganci domin 'yan baya. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China