Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba ta taba dakatar da taimakawa Afirka ba a fannin wanzar da tsaro da zaman lafiya, in ji Wang Yi
2019-09-27 19:38:15        cri
Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce ko da wasa kasar Sin ba ta taba dakatar da tallafin da take baiwa kasashen Afirka a fannin tsaro da wanzar da zaman lafiya ba.

Mr. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin taron kwamitin tsaron MDD game da tsaro da zaman lafiyar Afirka, wanda ya gudana a zauren MDD.

Jami'in ya ce Sin da kasashen Afirka abokai ne, kuma 'yan uwa da suke hadin gwiwa da juna. Ya ce a yanzu haka, sama da jami'an wanzar da zaman lafiya Sinawa 2,000 ne ke cikin tawagogin MDD na wanzar da zaman lafiya, dake ayyuka a kasashen Afirka 5. Wang ya kara da cewa, Sin na tallafawa kasashen Afirka da dabarun sanin makamar aiki a fannin tsaro da tabbatar da zaman lafiya.

Ya ce a watan Satumbar shekarar 2015 ne, Sin ta sanar da kafa wani asusun bunkasa tsaro da zaman lafiya da hadin gwiwar MDD, wanda ya mayar da hankali ga sha'anin tallafawa ayyukan wanzar da zaman lafiya, da yaki da ta'addanci, da wanzuwar ci gaba mai dorewa a Afirka.

Mr. Wang ya kuma ce ya zuwa yanzu, akwai ayyuka 34 dake da nasaba da Afirka, wadanda aka kaddamar da wannan asusu, matakin da ya sanya asusun zama dandali irinsa na farko na taimakawa nahiyar, na hadin gwiwar sassa 3, wato Sin da Afirka da MDD. Bugu da kari, Sin za ta ci gaba da tsaiwa tsayin daka tare da kasashen Afirka, a turbar su ta neman ci gaba cikin lumana. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China