Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakatariyar MDD tana shirin rage fitar da hayakin da ya kai kaso 45%
2019-09-23 09:27:36        cri
Sashen sadarwa tsakanin kasa da kasa karkashin sakatariyar MDD a jiya Lahadi ya fitar da sanarwar cewa, sakatariyar ta zartas da wani shiri na tsawon shekaru 10, inda ake sa ran za a rage fitar da hayakin da zai iya haifar da dumamar yanayi da kaso 45% ya zuwa shekarar 2030.

Sanarwar ta ce, an zartas da wannan shiri gabanin taron kolin MDD kan matakan tinkarar sauyin yanayi. Sabo da haka, sakatariyar na shirin rage yawan wutar lantarki da kowane mutum ke amfani da ita da kaso 20% kafin shekarar 2025, ya zuwa shekarar 2030 kuma, za a rage adadin da kaso 35%.

Yawan hayakin dake haifar da dumamar yanayin da sakatariyar MDD ke fitarwa ya kai kaso 58% na yawan hayakin da sassan MDD ke fitarwa gaba daya.

Sakatariyar na daya daga cikin manyan hukumomi shida na MDD, kuma ita ke da ma'aikatanta mafi yawa cikin hukumomin MDD. Ban da hedkwatar MDD da ke New York, sakatariyar tana da ofisoshi a biranen Geneva da Vienna da kuma Nairobi.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China