Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta karrama jami'ai 34 da suka taimaka wajen farfado da zaman lafiya a Somalia
2019-10-01 09:12:22        cri

Rundunar wanzar da zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afrika AU, wanda ke aiki a Somalia (AMISOM), ya karrama dakarun wanzar da zaman lafiya 34 dake aiki a hedkwatarsa dake Mogadishu, saboda gudunmuwar da suka bayar na taimakawa cimma burin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Somalia.

Kwamandan shirin AMISOM Tigabu Yilma ne ya bada lambobi da takardun shaidar karrama jami'an.

Dakarun da aka karrama, sun hada da na kasashen Benin da Burundi da Djibouti da Masar da Habasha da Ghana da Kenya da Uganda da Zambia da Zimbabwe da Birtaniya.

Tigabu Yilma, ya ce jami'an sun yi gagarumin tasiri wajen taimakawa rundunar cimma burinta, ta hanyar sadaukarwar da suka yi, musammam wajen yakar kungiyar 'yan ta'adda ta al-Shabab, lamarin da ya sauya rayuwar al'ummar Somalia.

Dakarun Somalia da na AU sun kasance suna yakar 'yan kungiyar al-Shabab a yankunan tsakiya da kudancin kasar, amma har yanzu mayakan na rike da wasu wurare a yankunan, inda suke dasa bama-bamai a kan titi da yi wa dakarun kwantar bauna.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China