Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci a karfafa hukumomin zaben Afrika
2019-09-04 10:38:29        cri

Wani jami'in kungiyar tarayyar Afrika (AU) ya bukaci a karfafa matsayin hukumomin zabe a kasashe Afrika.

Khabele Matlosa, daraktan sashen al'amuran siyasa na kungiyar ta AU ya ce, rashin tabbas game da tsarin gudanar da zabuka yana daya daga cikin dalilan da suka kashe gwiwar masu zabe wajen rashin fitowa a yayin zabuka da dama da aka gudanar a kasashen Afrika. Ya kara da cewa, wasu 'yan kasa da dama suna jin cewa ba'a yin la'akari da kuri'unsu yayin fitar da sakamakon karshe na zabuka.

Jami'in ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar yayin taron wuni biyu na shugabannin hukumomin zabe na nahiyar wanda aka gudanar a birnin Kigali, babban birnin kasar Rwanda.

Ya ci gaba da cewa, kwarin gwiwar da masu zabe ke da shi kan jam'iyyun siyasa da zabuka ta yi matukar raguwa. Tsarin gudanar da zabe muhimmin al'amari ne wajen shawo kan matsalolin rikice-rikice a nahiyar.

Shugaban hukumar zaben kasar Rwanda Kalisa Mbanda ya ce, muddin jama'a sun samu shugabanci na gari, sun kuma samu damar shiga a dama da su a harkokin gwamnati, sai za su goyi bayan tsarin gudanar da zabe. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China