Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci amfani da fasahar kirkire kirkire wajen magance matsalolin yara mata miliyan 53 na Afrika da ba sa makaranta
2019-08-29 10:14:05        cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta sanar a jiya Laraba cewa adadin yara mata da matasa mata miliyan 53 na Afrika da ba sa makaranta suna bukatar a samar musu da wasu damammakin amfani da fasahar zamani wajen warware matsalolin dake addabar rayuwarsu da kuma cimma burikansu na rayuwa.

Kungiyar ta Afrika na mambobin kasashe 55, cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, ta jaddada cewa, bunkasuwar fannin fasahar zamani ta samar da damammaki masu yawa da za su iya kyautata rayuwar yara mata da matasa mata wajen inganta kwarewar da suke da ita da basirarsu don samar musu da sana'o'in dogaro da kai wadanda za su warware matsalolin da suke tunkararsu, wannan hakki ne dake rataye a wuyan kasashe masu karfin fasahar kirkire kirkire. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China