Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU za ta kara hada kai da kasar Sin ta fuskar rage hasarar hatsi
2019-09-19 14:23:00        cri

An kira taron samar da abinci a hedkwatar kungiyar tarayyar Afirka (AU) dake Addis Ababa fadar mulkin Habasha, inda mahalarta taron da suka hada da wakilan kungiyar tarrayar Afrika AU da na kasar Sin suna ganin cewa, akwai bukatar sassan biyu su hada kai ta fuskar rage hasarar hatsi.

Wata jami'ar kula da harkokin aikin gona da raya kauyuka na AU ta nuna cewa, yawan 'yan Afrika zai kai biliyan 2.5 a shekarar 2050, hakan ya sa za a fuskanci matsalar karancin abinci. Saboda haka ne, AU take kokarin hada kai da kasar Sin a wannan fanni. Ta kara da cewa, Sin ta samu ci gaba mai armashi a fannin kawar da talauci da raya aikin gona, ban da wannan kuma, Sin na da kwarewa wajen samar da abinci da sarrafa amfanin gona da sauransu, ya dace kasashen Afirka su yi koyi da kasar.

Mataimakin shugaban kwalejin nazari na hukumar adana kayayyaki da hatsi na kasar Sin Zhang Yongyi shi ne ya jagoranci tawagar kasar Sin a taron da aka yi a wannan rana, inda ya bayyana cewa, Sin tana rabawa sauran kasashen Afrika fasahohi da kimiyyar rage hasarar hatsi, matakin da zai gaggauta zurfafa hadin kai da samun ci gaba mai kyau a wannan fanni a tsakaninsu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China