Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yi maraba da karin matakin dakile ta'addanci a yankunan tafkin Chadi
2019-09-30 11:50:00        cri
Ofishin kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar AU, ya jinjinawa shirin kasashen dake makwaftaka da tafkin Chadi, na aiwatar da karin ayyukan kakkabe ta'addanci.

Kwamitin wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya yi maraba da hadin gwiwar kasashen yankin, da hukumar zartaswar kungiyar AU, karkashin tsare tsaren hukumomin yankin da suka jibanci samar da daidaito, da farfado da yankuna, da dakile tasirin ayyukan Boko Haram a yankunan da hakan ya shafa.

Kazalika ya nuna yabo, game da matakin kasashen nan na G5 dake yankin Sahel na yaki da ta'addanci, wanda suka amince da shi yayin taron musamman na shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS.

Kwamitin na AU ya ce, alkawarin samar da kudi har dalar Amurka biliyan daya domin yaki da ayyukan ta'addanci, wanda taron shugabannin ya amince da shi a taronsa na ranar 14 ga watan nan abun a yaba ne.

Yankin tafkin Chadi, da ya kunshi kasashen Najeriya, da Chadi, da Kamaru da Jamhuriyar Nijar, ya sha fama da ayyukan ta'addanci daga mayakan Boko Haram, kasancewarsa yankin da mayakan suka fi kaddamar da hare-harensu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China