Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yi ta'aziyyar mutuwar Mugabe
2019-09-08 17:05:26        cri
Tarayyar Afrika AU, ta bayyana ta'aziyyar rasuwar tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe.

Cikin wata sanarwa, shugaban hukumar AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana jimami da ta'aziyyar mutuwar Robert Mugabe ga iyalansa da al'ummar kasar, a madadin daukacin Tarayyar Afrika.

Ya ce Tarayyar na jimamin mutuwar gwarzo, cikakken dan Afrika mai fafutukar 'yanci da dunkulewar nahiyar.

Marigayi Robert Mugabe ya tsunduma harkokin siyasa ne a shekarun 1960, a lokacin da ya kafa jam'iyyar ZANU a shekarar 1963 domin yaki da mulkin mallaka na Turawa.

Bayan Zimbabwe ta samu 'yancin kai daga Birtaniya a 1980, Mugabe ya zama Firaministan kasar har zuwa 1987, lokacin da koma Shugaban kasa, mukamin da ya rike har zuwa lokacin da aka hambarar da shi a shekarar 2017. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China