Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Sin ya gana da shugaban AU
2019-09-25 11:20:42        cri
Mamban majalisar gudanarwar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU, Moussa Faki, yayin da yake halartar babban taron MDD da ke gudana a birnin New York na kasar Amurka.

Wang Yi ya ce, karkashin jagorancin kungiyar AU, an kafa yankin ciniki cikin 'yancin a nahiyar Afirka a watan Yulin bana, wanda ya kasance muhimmin ci gaba cikin dunkulewar kasashen Afirka. Ya ce a bana ake cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyyar jama'ar kasar Sin, kuma Sin tana fatan karfafa dunkulewar Sin da Afirka bisa fahimta da goyon bayan juna.

Haka kuma, Wang Yi ya ce, a halin yanzu, ana fuskantar sauye-sauye da kalubale da dama cikin harkokin kasa da kasa, musamman ma a fannin kariyar ciniki da ra'ayin bangaranci da sauransu. A don haka, ya kamata a hada gwiwa yadda ya kamata domin kare ikon kasashe masu tasowa, da kuma tabbatar da adalci cikin harkokin kasa da kasa.

A nasa bangare kuma, Moussa Faki ya ce, cikin shekaru 70 da suka gabata, Sin ta sami ci gaba kwarai da gaske, ta kuma cimma nasarorin da ba a taba cimmawa ba, sabo da kokarin da shugabanni da jama'ar kasar suka yi. Ya ce kungiyar AU na yabawa shawarar ziri daya da hanya daya da Sin ta fidda, kuma ta na mata godiya matuka game da goyon baya da take baiwa kasashen Afirka, ciki har da aikin hana yaduwar cutar Ebola. Moussa Faki ya kara da cewa, ana fatan ci gaba da zurfafa dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, domin ba da karin tallafi ga jama'ar sassan biyu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China