Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Sin sun gabatar da kwandon furanni ga jaruman kasa
2019-09-30 13:34:18        cri

Ranar 30 ga watan Satumba rana ce ta "tunawa da shahidai" bisa dokar kasar Sin. Yau da safe ne, aka yi bikin gabatar da kwandunan furanni ga jaruman kasa ta Sin a filin Tiananmen dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da wasu shugabannin Jam'iyyar Kwaminis da na gwamnatin kasar Sin, da wasu wakilan jama'ar kasa kimanin dubu 4 sun halarci wannan biki, inda suka nuna girmamawa ga jaruman kasa a madadin daukacin al'ummar kasar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China