Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya mika wasikar murnar cika shekaru 60 da gano wurin hakar mai na Daqing
2019-09-26 15:46:06        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika wasikar murnar cika shekaru 60 da gano wurin hakar mai na Daqing, ga ma'aikatan dake aiki a wurin, da tsofaffin ma'aikatan da iyalansu a madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin.

A ranar 26 ga watan Satumba na shekarar 1959, bayan gudanar da bincike, aka gano wurin hakar mai na Daqing. A cikin shekaru 60 da suka gabata, yawan man da aka samu daga wurin ya kai ton biliyan 2 da miliyan 390, wanda ya samar da babbar gudummawa ga tsarin masana'antun mai na kasar Sin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China