Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada bukatar ci gaba da zamanantar da tsarin shugabanci da shari'a na Sin
2019-09-25 12:42:58        cri

Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping, ya jaddada bukatar ci gaba da ingiza zamanantar da karfin tsarin shugabanci da shari'a na kasar.

Xi Jinping ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi yayin da yake jagorantar zaman nazari na hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, game da kafawa da samar da sabon tsarin shugabanci da harkokin shari'a a kasar Sin.

Shugaban ya ce, tun bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, shekaru 70 da suka gabata, ake ci gaba da samar da tsarin gurguzu da shari'a mai hallayar musammam ta kasar Sin a hankali.

Ya ce, ya kamata daukacin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ta ci gaba da bin daidaitacciyar hanyar da aka tsara.

Ya kuma bayyana cewa, an samar da tsarin gurguzu mai halayyar musammam ta kasar Sin ne bisa dadewa da aka yi ana gudanar da shi da kuma bincike, wanda ya alamta wani gagarumin abu da aka samar a tarihin dan Adam.

Shugaba Xi, ya ce sabon tsarin gurguzu da JKS ta kafa, ya ba kasar damar samar da ci gaban tattalin arziki na ban mamaki da kuma kwanciyar hankali mai dorewa, sannan ya ba da sabuwar dama ga kasashe maso tasowa na tafiya da zamani. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China