Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin kasar Sin za su halarci bikin tuna da mazajen jiya
2019-09-28 16:50:52        cri

A bana ake cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar Jama'ar kasar Sin. Sa'an nan ranar 30 ga watan da muke ciki, ita ce ranar da aka kebe musamman domin tunawa da mazan jiya, wadanda suka sadaukar da kansu a fafutukar 'yantar da al'ummar Sinawa.

A wannan rana mai muhimmanci, wato gata Litinin, shugaban kasar Sin mista Xi Jinping, tare da sauran manyan kusoshin kasar, gami da wakilan al'ummar kasar daga sassa daban daban, za su je filin Tiananmen dake tsakiyar birnin Beijing na kasar, inda za su aza furanni a gaban dutsen tunawa da mazan jiya.

Zuwa lokacin, babban gidan telabijin da na rediyo wato CMG na kasar zai watsa labarai dangane da bikin kai tsaye daga filin na Tiananmen. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China