Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya taya kungiyar wasan kwallon raga ta mata ta kasar Sin murnar zama ta farko a gasar WWC
2019-09-29 20:49:49        cri
Kungiyar wasan kwallon raga ta mata ta kasar Sin ta zama zakara a gasar cin kofin duniya ta kwallon raga ta mata ta shekarar 2019. Game da haka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna da gaisuwa, ga dukkan 'yan wasan kungiyar da masu horar da su.

Xi Jinping ya jaddada cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 70 da kafa sabuwar kasar Sin, kuma sabuwar kasar ta cimma gaggaruwar nasara sakamakon hadin kai a tsakanin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da jama'ar kabilu daban daban na kasar. Haka zalika Xi ya yi fatan kungiyar kwallon raga ta matan za ta ci gaba da kokari don kara samun sakamako mai kyau. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China