Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya gabatar da lambobin yabo da na karramawa na kasar
2019-09-29 16:08:59        cri

 

 

Shugaban kasar Sin, Xi Jinping, ya gabatar da lambaobin yabo da na karramawa na al'ummar jamhuriyar kasar Sin, a safiyar yau Lahadi a babban dakin taron jama'a na kasar.

Da yake jawabi, Shugaba Xi Jinping ya taya gwaraza da wadanda suka zama abun koyi da suka karbi lambobin yabon da kuma bakin da suka samu lambobin karramawa na abota murna.

Ya ce wadanda aka karrama wakilan jama'a ne da suka bada gudummawa ga burin JKS da na jama'a, yana mai cewa, ayyuka da gudummawarsu, za su ci gaba da kasancewa cikin tarihin kasar Sin.

Ya ce idan aka karrama tare da yayata gwaraza, to za a samu karin irinsu a nan gaba, inda ya ce JKS da gwamnatin kasar, suna daukar batun girmama gwaraza da masu bada gudummawa da muhimmanci.

Ya karfafawa wadanda aka karrama gwiwar ci gaba da girmamawa da yin kyakkyawan tasiri kan al'umma da irin karfin halin da suke da shi.

Ya kara da yin godiya matuka ga wadanda suka samu lambobin karramawa ta abota, saboda gudunmuwar da suka bayar ga ci gaban kasar Sin, yana mai cewa, a shirye al'ummar Sinawa suke su hada hannu da 'yan kasashen waje, wajen samar da al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama tare kara kyautata yanayin duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China