![]() |
|
2019-09-25 10:13:48 cri |
Yayin wani taron manema labarai, mataimakin shugaban hukumar, Ning Jizhe, ya ce a tsakanin wancan lokaci, kudin shigar kowanne dan kasa, ya karu sau 70, daga yuan 119, kwatankwacin dala 16.8, zuwa yuan 64,600.
Jami'in ya ce kasar Sin ta samu ci gaba zuwa kasa ta 2 mafi karfin tattalin arziki a duniya, kuma kasar da ta fi kowacce a fannin cinikayyar kayayyaki. Haka zalika ita ce kasar da tafi kowacce mallakar dukiya mai yawa a asusun ajiya na ketare, kana kasa ta 2 mafi cinikayyar hidimomi da amfani da jarin kasashen waje, har ila yau, kasa ta biyu mafi zuba jari a kasashen waje.
Ya kara da cewa, cikin shekaru 70 da suka gabata, yawan jarin da kasar Sin ta zuba ta fannin kadarori na ci gaba da habaka cikin sauri, wanda ke kara bunkasa ayyukan gona da kayayyakin aiki a masana'antu da kuma ababen more rayuwa. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China