![]() |
|
2019-09-30 09:44:25 cri |
A safiyar gobe 1 ga watan Oktomba, bisa agogon birnin Beijing na kasar Sin, za a gudanar da gaggarumin taron taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, a filin Tian'an'men dake tsakiyar birnin Beijing. Inda babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin soja na kasar Sin Xi Jinping, zai gabatar da jawabi ta telibiji, sannan kuma za a gudanar da faretin soja, da jerin gwanon jama'a.
Gidan radiyo, da gidan telibijin, da shafin yanar gizo na Intanet, za su watsa labarai kai tsaye, game da wannan gaggarumin taro, da faretin soja, da jerin gwanon jama'a. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China