Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da bikin nune-nunen nasarorin da aka samu ta fannin harkokin dabi cikin shekaru 70 tun bayan kafuwar jamhuriyar jamaar Sin
2019-09-23 16:33:40        cri

A yau Litinin ne, aka kaddamar da bikin nune-nunen nasarorin da aka samu ta fannin harkokin dab'i a cikin shekaru 70 da suka wuce, a yayin da ake murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, bikin da ya gudana a gidan nune-nunen harkokin dab'i na kasar Sin. Za a gudanar da bikin har zuwa karshen watan Oktoba, inda aka baje kolin takardu da littattafai da jaridu sama da 80. Har wa yau, an ware sashe na musamman na nune-nunen littafi mai taken "bayanin Xi Jinping a kan harkokin tafiyar da mulki" da aka fassara shi cikin harsunan waje daban daban.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China