2019-09-26 09:40:44 cri |
Tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, aka tsai da shirin kokarin raya kimiyya da fasaha, zuwa ga gudanar da tsarin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, inda aka mai da kimiyya da fasaha matsayin karfi mai tushe na samar da kayayyaki. Kana kuma, daga shekaru 90 na karni na 20, Sin ta fitar da tsarin raya kasa ta hanyar kimiyya da ilmi, kuma har zuwa yanzu, ana dora muhimmanci sosai kan karfafa kasar Sin don zama kasa mafi karfi a fannin kimiyya a duniya. Sin na nacewa ga yin kirkire-kirkire cikin 'yanci da kara ba da tabbaci ga ikon mallakar ilmi. Tattalin arzikin Sin na samun bunkasuwa cikin sauri bisa karfin yin nazari da kirkire-kirkire mai inganci, da sabbin kimiyya da fasahohi, sabbin albarkatu da fitar da sabbin kayayyaki da sauransu. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China