Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: An gudanar da bikin nuna fasahohi gabanin bikin cikar Jamhuriyar kasar shekaru 70 da kafuwa
2019-09-30 10:51:45        cri
A jiya Lahadi ne aka gudanar da wani gagarumin biki, na nuna fasahohi a dakin taruwar jama'a dake nan birnin Beijing, gabanin bikin cikar jamhuriyar kasar shekaru 70 da kafuwa.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da firaminista Li Keqiang, tare da wasu jama'a da yawansu ya kai 4,000 sun ganewa idanunsu yadda bikin ya gudana.

An dai raba bikin kashi 4, inda kashi na farko ke kunshe da bayanai game da yadda kasar Sin ta yi fafutukar fita daga kangi, da yadda JKS ta hade kan kasar, matakin da ya kai ga kafuwar sabuwar jamhuriya bayan shekaru 28.

Kashi na biyu na bikin kuwa, na kunshe ne da juyin juya halin gurguzu, bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin a shekarar 1949. Sai kuma kashi na 3 mai kunshe da ci gaban da kasar Sin ta samu, tun bayan fara aiwatar da manufofin gyare gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da ma yadda al'ummar Sinawa suka sanya burin hadin kan kasa a gaba.

Kashi na 4 kuwa na wannan biki, ya kunshi ci gaba da salon gurguzu mai halayyar musamman na kasar Sin ya haifar, a gabar da aka shiga sabon karni tun daga taro na 18 na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin.

An dai gudanar da wakoki salo salo, da bayanai a yayin wannan biki. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China