Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta harba tauraron Bil Adama samfuri ZY-1 02D
2019-09-12 14:12:10        cri

Yau Laraba da misali karfe 11 da mintoci 26 na safe agogon wurin, Sin ta harba tauraron Bil Adama samfurin ZY-1 02D daga cibiyar harba tauraron Bil Adam ta Tai Yuan, bayan harba shi, tauraron ya kama hanyarsa kamar yadda aka tsara, matakin da ya alamta cewa, Sin ta yi nasarar harba shi. Wannan tauraro zai hade da sauran taurarin da za a harba, don ba da tabbaci ta fuskar sadarwa kan aikin sarrafa albarkatun hallitu da kula da muhalli, tare da ba da gudunmawa wajen kandagarki bala'u daga indallahi, da kiyaye muhalli, da raya birane da kauyuka da kula da harkokin ko ta kwana da sauransu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China