Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Times Higher Education ya gabatar da jerin sunayen nagartattun jami'u a duniya
2019-09-12 14:20:44        cri

Jiya Talata, Times Higher Education wato THE a takaice ta gabatar da jerin sunayen nagartattun jami'o'in a duniya na shekarar 2020, a karon farko jami'ar Tsinghua da Peking sun zo na farko da na biyu a Asiya.

Rahotanni na cewa, nagartattun jami'o'in babban yanki sun samu maki mai kyau ta fuskar samun karbuwa da yawan kudin shiga cikin ayyukan nazari, matakin da ya bayyana gudunmawar da gwamnatin kasar Sin ke baiwa sana'ar ba da ilmi. Sin na nuna hazaka sosai ta fuskar yin nazari da ba da ilmi, idan an kwatanta da sauran jami'o'i 200 wadanda suke sahun gaba a duniya, amma har yanzu sun yi koma baya a fannin dunkulewar kasa da kasa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China