Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin jakadancin Sin a Nijeriya ya kira liyafar murnar cika shekaru 70 da kafuwar kasa ta Sin
2019-09-27 10:56:49        cri

Jiya Alhamis, jakadan kasar Sin dake kasar Nijeriya Zhou Pingjian ya kira wani liyafa a ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar, domin taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

Zhou Pingjian ya ce, cikin wadannan shekaru 70 da suka gabata, kasar Sin ta canja kwarai da gaske, ta kammala ayyukan neman ci gaba cikin wadannan shekaru kamar yadda kasashe masu ci gaba suka yi cikin shekaru sama da dari. Ya ce Sin ta samu gaggarumin ci gaban ne bisa jagorantar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, wadda ta tsara wata hanyar neman ci gaba da ta dace da halin da Sin take ciki.

Ya kuma kara da cewa, Sin da kasashen Afirka na da kaykkyawar makoma ta bai daya. Kasar Sin tana goyon bayan kasar Nijeriya wajen neman hanyar ci gaba da ta dace da halin da kasar take ciki, kana tana son karfafa fahimtar juna dake tsakanin kasashen biyu da kuma aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" cikin hadin kai, da aiwatar da sakamakon taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing yadda ya kamata, da nufin ba da taimako ga kasar Nijeriya wajen raya tattalin arzikinta da kuma daga dangantakar abota dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

Wakilin gwamnatin tarayya, kana ministan harkokin wajen kasar Nijeriya Zubairu Dada ya mika sakon taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar kasar Sin a madadin shugaban kasar Nijriya Muhammadu Buhari da gwamnatin kasar. Yana mai cewa, ana gudanar da dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Nijeriya a fannoni daban daban, da suka hada da mu'amalar shugabannin biyu da hadin gwiwar kasashen biyu mai kyau a fannonin ciniki da tattalin arziki, kuma Nijeriya tana mai da hankali sosai kan zamuncin dake tsakaninta da Sin.

Haka kuma, ya ce Nijeriya ta riga ta sa hannu kan takardar fahimtar juna game da shawarar "ziri daya da hanya daya", wato ta shiga cikin babban iyali na "shawarar ziri daya da hanya daya", kuma tana fatan Sin da Nijeriya za su ci gaba da karfafa hadin gwiwarsu a fannin ciniki da tattalin arziki. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China